***Alhamdu lillah***
*****LITTAFINA NA FARKO, LITTAFIN DA NA FI SO*****
Ina farin cikin sanar da ku cewar a yau ne ranar 1th-Muharram-1438 na wallafa littafina BAN SAN SO BA. Littafine da ke kunshe da ban dariya da ban tausayi, sannan akwai darasi wanda nake fatan makarantana zasu amfana da shi. Na sadaukar da wannan littafi ne ga Matata, kar ku tambayeni sunanta domin amsar itace nima ban santaba na sadaukar mata ne kawai domin na nuna mata irin tsantsar son da nake yi mata tun kafin na san ko wacece. Karfa kuce na fiya zumudi idan kuma na mutu banyi aure ba fa? Wannan hukunci ne na ubangiji amman ni dai na sadaukar da littafin ga Matata ko da kuwa ban yi aure a duniya ba zan ba matata ta gidan aljanna labarin na sadaukar mata da wani littafi mai dadi a duniya.
Ina son na kara amfani da wannan damar domin na mika dumbin godiya ta ga ‘yan uwana da abokan arziki wanda bazan manta da irin taimakon da kuke bani ba Allah ya saka muku da gidan Aljannar fiddausi tare da ni.
***Alhamdu lillah*** *****My First Book, My best Book***** I am indeed very delighted to inform you that today 1th-Muharram-1438 I published my book BAN SAN SO BA. Is a prose that contains both tragedy and comic roles, it has a moral lessons that I wish my readers will understand and benefit. I dedicate the book to my wife, don’t ask me who she is because my answer is I don’t know. I wish to use this opportunity to send my regard to both my Family and Friends for all their contribution in fact I appreciate all your concern my Allah reward you with Jannatul Fiddaus together with me.
“Abubakar!” Mama ta kirani na juya jikina a sanyaye na amsa, “na’am Mama” “karka manta wannan karon zaka fuskanci Saudah ne a matsayin matar da za ka aura ba matsayin kanwa kamar yadda ka dauketa a baya ba” Na gyada mata kai cikin nuna karfin gwiwa ba tare da na yi magana ba ta nunamin alamun na tafi na juya na nufi hanyar da za ta mayar da ni babban falon gidan inda na tarar da Saudah a zaune ta zubawa kofar dakin Mama ido bata ko kiftawa wanda hakan ya tabbatarmun da ni ta ke jira. Na yi murmushi lokacin da na karasa wajenta tana zaune a kan doguwar kujera don haka na samu waje a kusa da ita na zauna. Na juya na fuskanceta da zummar yi mata magana sai kuma maganar Mahaifiyata ta fadomun. “...ina son a cikin wadannan kwanakin ka nemi soyayyar Saudah ta amince da kai a matsayin mijin da za ta aura...” Wani tattausan murmushi ne ya su6ucemun wanda ban san lokacin da na yi shi ba. Ni da BAN SAN SO BA ta ya zan iya neman soyayyar mace har ta amince da ni a cikin kwana uku? “tunanin me ka ke yi Yayana?” Saudah ce ta katsemun tunanin da na ke yi ta hanyar yimun magana. Na kalleta har a lokacin da sauran guntun murmushin a kan fuskata na ce, “bakomai kanwata wata magana ce ta fadomun shi ne abun ya bani dariya” Saudah ta yi murmushi sannan ta ce, “nima fadamun na ji ka ji Yayana” Na zazzaro ido ina kallonta na ce, “ke sirri ne ba a son kowa ya ji” Cikin shagwa6a Saudah ta ce, “Yayana daman yanzu har a kwai wani sirri da za ka iya 6oyemun?” na girgiza mata kai domin na gajarce tsayin surutun nata domin ta fara takuramun sannan na ce, “yanzu dai je ki kawomun lemo mai sanyi na sha sai mu yi zancen” Saudah ta yi murmushi sannan ta tashi ta nufi hanyar kitchen domin daukomin lemon kamar yadda na umarceta. Nikuwa daman na yi mata haka ne saboda ta tafi ni kuma na samu damar guduwa domin ina son kadaici, idan na ce ta kyaleni ba zata kyaleni ba ta cika takura ga surutu. Sai da na bari ta shiga kitchen din sannan na tashi da sauri na fita. Ummi ta bini da kallo tana dariya daman ta fahimci so na ke na gudu. Ban tsaya sauraronta ba ina ji ta na cewa “a dawo lafiya” na fita da sauri na shiga motata na tasheta na fita daga cikin gidan. Wajen gefannin magriba na farka daga nannauyan barcin da nake na shiga bandaki na yi wanka na dauro alwala sannan na fito na saka doguwar riga na tafi masallaci bayan mun idar da sallar magriba na shiga gida inda na tarar da Ummi da Saudah a zaune a cikin falon da hawaye kwance a kan fuskar Saudah wanda na kasa fahimtar na mene ne. “lafiya Ummi me a ka yi wa Beauty ta ke kuka?” Na tambayi Ummi lokacin da na karasa wajen da suke zaune na kurawa Saudah ido ina kallonta tamkar ina son gano dalilin kukanta. Ummi ta waigo ta kalleni da alamun damuwa a kan fuskarta ta ce, “tafiyar da ka yi dazu ka barta shi ne abun har yanzu be wuceba na bata hakuri ta ki hakura” Na dan yatsina fuska ina kallonta na ce, “kin san kyawawan mata da sharri yanzu so ta ke Mama ta fito ta zaci dukanta na yi” Kamar na tashi injin mota na ji Saudah ta bude baki cikin siririyar muryarta ta fara yin kuka. Gabana ya yi mummunan faduwa lokacin da na tuno kwana uku Mahaifiyata ta bani na janyo hankalinta ta amince da ni a matsayin mijin da zata aura amman halina be canzaba gashi na sata kuka kamar yadda na saba. Da sauri na kalleta a yunkurina na kwantar mata da hankali na ce, “in banda abinki Saudah tsabar shagwa6a sai kace wata karamar yarinya dan na fita ba tare da ke ba sai ki samu waje ki 6are baki kinawa mutane kuka” A tsammanina Saudah za ta yi shiru domin dadadan kalaman da na tarairayeta da su amman sai na ji ta kara bude murya sautin kukanta ya karu fiye da na baya. “dan Allah Aunty Saudah ki yi hakuri kar Mama ta zo ta ganki kina wannan kukan kin san yanzu zata fito lokacin cin abinci ya yi” Ummi ce ta fara yiwa Saudah magana lokacin da ta fahimci hankalina ya tashi da irin kukan da ta ke yi wanda ta tambata tsoro na ke ji kar ran Mahaifiyarmu ya 6aci. Saudah ba ta daina kukan da ta ke ba duk da hakurin da Ummi ta bata wannan ne ya sa ni canza salon rarrashina na kirkiri murmushin karfin hali a kan fuskata sannan na fara yi mata magana cikin kwantar da murya. “yi shiru, yi shiru Saudah, yi shiru baiwar Allah, yi shiru ‘yar aljanna” kara fashewa tayi da kuka, wannan karan har da sautin murya wanda nasan Mama ta na jin kukan zata fito domin ganin abun da ke faruwa. “Saudah!” Na kira sunanta cikin wata sassanyar murya domin canja salon lallashina, ta dago kai ta kalleni da dara daran fararen idanuwanta masu haske kamar madara wanda lokaci daya suka rikide zuwa ja saboda kukan da ta ke yi. “yakamata ki daina kukannan da ki ke dan kar Mama ta zo ta zaci dukanki na yi, kinga wannan kukan sharri ne da makirci irin naku na Mata...” Takun tafiyar Mama da muka jiyo ta doso falon ne ya sa muka mike ni da Ummi da sauri muka 6oye Saudah a bayanmu fuskokinmu suna bayyana alamun tsoro. “lafiya na ke jiyo kamar kukan ‘yata Saudah, ba dai kai ka doketa ba ko Abubakar?” Mama ce ta watso mana wannan tambayar lokacin da tashigo falon tana dube dube domin ba ta ga Saudah ba saboda mun sata a tsakiya ni da Ummi mun 6oyeta a bayanmu. “kuka kuma Mama?” Daddadar muryar Saudah na jiyo daga bayanmu tana tambayar Mama. Na juya a dan tsorace na kalleta muka hada ido ta sakarmun wani tattausan murmushi tare da yin fari da dara daran idanunta masu kyawun launi sannan ta mayar da kallonta kan Mama lokacin da ta ke karasowa wajen da muke ta ci gaba da cewa, “nifa yanzu Yaya Abubakar ya ce na kawo mishi lemo mai sanyi zai sha” ta danyi shiru tana satar kallona ta gefan ido ta ce, “ko Yayana?” Da sauri na daga mata kai na ce muryata tana rawa alamomin rashin gaskiya suka bayyana a kan fuskata na ce, “haka ne kanwata amman tunda Mama ta fito ki barshi kar ta ce na fiya takura miki” Mama ta yi murmushi ta ce, “ni ban ce ba. Yi sauri ki je ki kawowa yayanki lemon da ya ke so ki dawo mu ci abinci ‘Yata” “to Mama” Saudah ta amsa mata da sauri ta juya ta nufi hanyar kitchen da murmushi bayyane a kan fuskarta. Na juya na kalli Ummi muna hada ido muka bayyana wata sassanyar ajiyar zuciya a tare wacce ta janyo hankalin Mama ta kura mana ido tana kallonmu sannan ta ce, “ku kuma lafiya ku ke yin wannan ajiyar zuciya kamar marasa gaskiya?” “a’a babu komai Mama” Na amsa mata a dabarbarce muryata tana sarkewa sannan na ci gaba da cewa, “mu karasa wajen cin abincin kafin ta fito ko Mama”
minti daya biyu sai na kalli Saudah ina ganin irin kallon da ta ke yi mun alamun tana son ta yi mun magana amman saboda hararar da na ke yi mata ta kasa furta abun da ke zuciyarta. Can na nutsu na bayar da hankalina gaba daya wajen kallon talabijin din na ji muryar Saudah tana kiran sunana. “Yaya Abubakar!” Ta kirani cikin sanyin murya. Na juya jikina a sanyaye na kalleta fuskata ba yabo ba fallasa na ce, “na’am kanwata” Ta danyi shiru alamun tana dan jin nauyin maganar da ta ke son fada sai kuma ta ce, “ina son mu koma can wajen dining mu zauna mu yi hira ka ji Yayana” Na hade rai tare da mayar da idanuna wajen kallon shirin talabijin din sannan na fara bata amsa ina magana fada-fada. “yanzu Saudah muna zaune ana kallo cikin ‘yan uwa sai ki ce mu koma gefe mu zauna mu yi hira saikace wasu munafukai, ni bazanje ba ina nan idan hira ki ke so ga Ummi nan ki dauketa ku je ku yi ai daman ni ba sa’anki ba ne...” Kallon da Mama ta watsomun ne ya sa sauran maganar ta makale a fatar bakina na yi saurin sunkuyar da kai kasa lokacin da na fahimci kuskurena domin an bani umarnin na nemi soyayyarta a cikin kwana uku amman gashi kwana daya yana neman shudewa ni ko a jikina duk maganar da ta zo bakina ya6amata na ke, daga safiya zuwa dare na 6ata mata rai ya fi a kirga. “tashi ka je” Mama ta bani umarni, jikina a sanyaye na tashi zan tafi wajen cin abincin da Saudah ta ce mu je mu yi hira na yi gaba ba tare da na jirata ba. “bazaka jirata ku tafi tare ba?” Mama ta yi mun magana lokaci daya na kame a wajen da nake kamar wani tsohon soja, Saudah ta taso tana tafiya a hankali ta karaso wajen da na ke ta ce, “mu je Yayana” Ba tare da na yi mata magana ba na yi gaba muka jera muna tafiya a hankali a lokacin na jiyo muryar Mama tanamun magana. “kuma ina son ka yi mata hira mai dadi wacce zata sata fara’a na dunga hango fararen hakoranta ina zaune daga nan” Jikina a sanyaye na ce, “to Mama” Na amsa mata a lokacin da muke karasawa wajen da zamu zauna ina jiyo muryar Ummi tanamun dariya domin ta san bani da kalaman da zan fadawa Saudah a wannan lokacin wanda zasu sata dariya da dai kuka a ka ce cikin mintina kadan zan sata domin na san duk wata hanya da ake bi idan ana son ganin hawayen Saudah.
“Assalamu alaikum” Na yi musu sallama lokacin da nake saka kafata ta dama a cikin babban falon gidanmu. Ba wanda ya amsamun, nima banyi tsammanin zan samu wanda zai amsamun ba duk da idanuna sun ganemun Abba da Momi a tsatstsaye a cikin falon rike da dogayen dorina masu kauri da tsayi. “sannu da zuwa” Momi ta ce mun lokacin da na tsaya nesa kadan da inda suke na sunkuyar da kaina kasa ina nazarin irin dukan da zan sha yau karon faro a rayuwata domin tunda nake ba’a ta6a dukanaba. “daga ina ki ke?” Muryar Momi na ji ta kara watsomun wata tambayar bayan da ta ji na yi shiru na kasa amsa mata sannu da zuwan da ta yi mun. Kamar yadda ban amsa mata tambayarta ta farko ba haka ta biyunma ban amsa mata ba domin ban san ta inda zan fara ba. Abba ne ya ja wata doguwar ajiyar zuciya sannan ya ce, “ai ba zata iya fada miki daga inda take ba, abun ne da kunya Ameela a hotel!” Yarrrrr! Na ji tsigar jikina ta tashi domin wannan ne karon farko da Mahaifina ya fara kirana da suna ‘Ameela’ wanda na tabbata ba zai wuce ya fara nadamar radamun sunan Mahaifiyarsa da ya yi ba. Jikina a sanyaye, zuciyata a karaye yayinda idanuna suka cicciko da hawaye na karasa gabansu na nutsugunna a tsakiyarsu na cire hijabin da ke jikina domin na basu damar dukana yadda ransu ya ke so duk da na san dukan ba zai yaye musu bakin cikin da na jefa zuciyoyinsu ba. Haka suka sa dorinar hannunsu suka dunga dukana tun ina iya jurewa har na cukwikwiye a waje daya na kare fuskata. mu”
Muryata a sanyaye na yi sallama lokacin da nake kokarin shiga karamin falon dake dakin Momi. “amin wa’alaiki assalam” Muryar Momi na ji ta amsamun sallamar da na yi dan haka na shiga ina tafiya a hankali kaina a sunkuye ina kallon kasa. “lafiya?” Muryar Momi na karaji a karo na biyu ta dakamun tsawa wanda na dan tsorata sannan da sauri na dago kai na kalleta jikina sai karkarwa yake na ce, “abinci na dafa na zo muci da Umaima” Wani dogwan tsaki Momi ta ja, ga wani kallo da takeyimun mai cike da nuna tsana da tsangwama ta cemun, “cemiki akayi Umaiman bataci abinci ba ne ko me?” Na yi shiru ba tare da na amsa mata tambayar da ta yi mun ba, hakan ne ya bata damar ci gaba da maganarta da cewa, “to ki fita ki bamu waje, ki je can ki ci kazantarki!” Rassss! Gabana ya fadi domin kalmar da Momi ta fadamun tana nuni ne da irin kyamar da take yimun. Wasu zafafan hawayene masu dumi suka saukomin zuwa kan kumatuna, na juya a hankali jikina a sanyaye zan fita daga cikin falon, har na juya sai na ji ina sha’awar na kalli Umaima wacce saboda sunkuyar da kan da na yi kasa tun shugowata falon bai sa na kalli inda takeba. Na daga kaina a hankali na kalleta, tana zaune ne akan karamar kujerar dake ajje a gefen Momi ta dora kafa daya kan daya, fuskarta ba alamun damuwa kamar yadda na tsammata, kallon kaskancin kawai da ta watsomun ya i’sa ya tabbatarmun da an fadamata laifin da na aikata, maimakon ta ji tausayina ta kusanceni domin na samu sanyi a cikin zuciyata itama sai ta biyewa iyayenmu ta nisanceni. Duniya kenan! Juyi-juyi, wataran a sha zuma, wataran a sha madaci. Daman mumini baya rabuwa da jarrabawar Ubangijinsa har sai ya koma gareshi. mu”
A kwana na bakwanne da yamma na samu saukin ciwon jikin da zazza6in dake damuna dan haka na yi wanka na gyara jikina sannan na tashi na dauki hijabina na saka na fita daga cikin dakina, kai tsaye na tattaka matattakalar bene kasancewar 6angaren Mahaifinmu yana saman benan gidanmu. A zaune na sameshi a falonshi da jarida rike a hannunshi yana karantawa. Na yi mishi sallama. Ya amsamun ciki-ciki ba tare da ya dauke kanshi daga karatun jaridar da yake yi ba, na samu waje a kasan kafet nesa kadan da inda yake zaune na zauna sannan na sunkuyar da kaina cikin ladabi na fara gaishe da shi amman shiru yaki amsawa. Wannan dalilin ne ya sa na fara yi mishi bayanin takamaiman abun da ya kawoni wajensa da cewa, “Abba na zo wajenka ne domin na nemi gafarar laifin da na aikata maka, sannan na fadama yadda abun ya faru domin ka yi mun hukunci dai-dai da laifin da na aikata maka” Wani irin kallo ya yi mun ta kasan tabaran da ke makale a kan fusarsa, ransa a 6ace ya fara yi mun magana. “karki sake na kara jin kalma daya ta fita daga bakinki, ki tashi ki fita ki bani waje, daga yau karna kara ganin kafarki a falo ko dakina in har kina son ki zauna lafiya a gidannan” “to Abba” Na amsa mishi jikina a sanyaye, ba abunda nake iya maimaitawa sai kalmar ‘inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un’ a cikin zuciyata. Idanuna suka ciko da kwalla, haka na tashi na fita daga cikin falon na sauko kasa, kai tsaye 6angaren Mahaifiyata na dosa ko na samu sauki da sassauci a wajenta, amman abun da Mahaifina ya fadamun itama shi ta fadamun cewar karna kara zuwa wajenta. Na kalli Umaima dake zaune a gefen Mahaifiyarmu nan da nan na ga idanunta sun ciko da kwalla alamun ta tausayawa halin da nake ciki kuma tana son ta taimakamun amman da alamar an yi mata sharadin kar ta kulani domin mikewa ta yi ta shige cikin dakin Mahaifiyarmu, ina jiyo shashshakar kukan da ta ke yi. “ki tashi ki 6ace ki ban waje!” Mahaifiyata ce ta dakamun tsawa lokacin da nake durkushe a gabanta kaina a sunkuye ina kuka ina rokonta ta yafemun. Ba shiri na tashi na fita daga dakin na doshi hanyar dakina ina tafiya ina jan kafa tamkar wata mai ciki saboda nauyin da kafafuna sukaimun. “ki lazumci karatun alqur’ani a duk lokacin da kika tsinci kanki a cikin halin tsanani da kuncin rayuwa, insha Allahu, Allah zai samiki nutsuwa da aminci a zuciyarki...” Shawarar da Abdulnoor ya bani ce ta fadomin lokacin da na ke shiga cikin dakina. Na shiga bandaki na dauro alwala sannan na zarce wajen da Alqur’anina da sallaya ke shimfide a karshen kuryar dakin na zauna tare da nutsuwa na mikawa Ubangiji dukkan lamurana, sannan na bude suratul fahita na fara karatuna cikin nutsuwa, bayan na idar da karantata na shiga suratul baqra. Cikin dan kankanin lokaci Ubangiji Allah ya yayemun dukkan damuwa da kuncin da nake ciki, na samu nutsuwa da aminci daga rabbil alamin. mu”
Gabana ya yi mumunar faduwa lokacin da idanuna suka hangoshi, sannan cikin sauri na yi bisimillah tare da fara karanto ayoyinnan biyu na karshen suratul baqra wanda manzon Allah ya fadi falala da tarin albarkar da ke tattare da su, na fara tafiya a hankula cikin sanyin jiki kaina ya na kallon kasa yayin da zuciyata ke dukan uku-uku domin na san ko zan mutu bazan iya furta mishi ina sonshi ba, hakanan idan na wuce bai tsayar da ni ba nanma mutuwar ce domin ban san yadda rayuwata za ta kasance ba in har na kuma rasashi a karona biyu. Har na wuceshi bai dago kai ya kalleni ba kamar yadda na tsammata yana zaune ya kurawa jaridar hannunsa ido. jikina ya yi sanyi zuciyata ta raunana, kafafuna suka fara sassarkewa kamar na mai koyan tafiya, kiris ya rage na fara zub da hawaye na jiyo zazzakar muryarsa tana rangadamun sallama. “assalamu alaiki” Duk da ban juya na ga mai yin sallamarba na san shi ne domin shi kadai zuciyata ta aminta da son jin muryarsa a wannan lokaci, shi kadai idanuna suke mararin gani a cikin samarin wannan zamani. “ameen wa’alaiaka assalam” Na amsa mishi sallamar da ya yi mun tare da juyawa a hankali inda idanuna sukai arba da shi a tsaye a bayana, a zahiri ba a mafarki kamar yadda na saba mafarkinsa ba, da wani tattausan murmushi bayyane a kan fuskarsa. Fari ne, dogo, kyakykyawa yana da yalwar gashin gira da ta kasumba, idanuwansa farare ne kal da farin tabarau sanye a kan fuskarsa. yana sanye cikin farar shadda dinkin doguwar riga da farar hula sanye a kanshi. Ya kara fadada murmushin kan fuskarsa lokacin da ya ga na tsaya ina kare mishi kallo sannan ya ce, “ki yi hakuri baiwar Allah na tsayar da ke a kan hanya ba tare da na nemi izinin yin hakan ba” Na mayar mishi da martanin tattausan murmushin da ya yi mun ina mai 6oye farincikin da ya mamaye zuciyata na ce, “karka damu, sallamar da ka fara yimun ta gamsar da ni domin ita ce kalmar da Manzon Allah (S.A.W) ya umarcemu da mu fara isar da ita yayin da muka hadu da junanmu”
na zo wucewa ta karkashin wata inuwa da aka tanada domin hutawar dalibai, kaina a sunkuye ya ke ina kallon kasa kamar yadda na saba a duk lokacin da nake tafiya, kamar ance na daga kaina na daga inda na yi ido hudu da wani saurayi a zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada domin hutawar dalibai. fari ne kyakykyawa ajin farko a cikin sahun samari da jarida rike a hannunsa. Rasssss! Gabana ya fadi yayin da bugun zuciyata ya canza ya fara bugawa da sauri da sauri. Wannan ne karon farko da na fara shiga irin wannan yanayi shiyasa ya zamomun bakon abu. Ga mamakina muna hada ido da shi sai na ga ya dauke idonsa kamar bai ganniba ya mayar da hankalinsa kan karatun jaridar da ya ke yi. Na kura mishi ido tare da rage saurin da na ke domin kar na wuce shi da wuri amman shi ko a jinkinsa tamkarma bai ga wata halitta mai kyau da dauke hankalin ‘ya’ya samari ba, halittar da duk wani saurayi da ya kalleta sai ya daga kai ya kara kallonta ko bai tankaba ya zama tarihi a cikin rayuwarsa cewar idanunsa sun ta6a kallon wata halitta mai kyau abar kwatance a cikin ‘ya’ya mata. amman ga mamakina yau sai ga shi na hadu da wanda ya canza bugun zuciyata ya sa kafafuna sassarfa amman shi ko a jikinsa ya mayar da hankalinsa kan karatun jaridar da ya ke yi tamkar idanunsa basa gani.
No comments:
Post a Comment