
***Alhamdu lillah***
*****My First Book, My best Book*****
I am indeed very delighted to inform you that today 1th-Muharram-1438 I published my book BAN SAN SO BA. Is a prose that contains both tragedy and comic roles, it has a moral lessons that I wish my readers will understand and benefit. I dedicate the book to my wife, don’t ask me who she is because my answer is I don’t know.
I wish to use this opportunity to send my regard to both my Family and Friends for all their contribution in fact I appreciate all your concern my Allah reward you with Jannatul Fiddaus together with me.
“Abubakar!”
Mama ta kirani na juya jikina a sanyaye na amsa,
“na’am Mama”
“karka manta wannan karon zaka fuskanci Saudah ne a matsayin matar da za ka aura ba matsayin kanwa kamar yadda ka dauketa a baya ba”
Na gyada mata kai cikin nuna karfin gwiwa ba tare da na yi magana ba ta nunamin alamun na tafi na juya na nufi hanyar da za ta mayar da ni babban falon gidan inda na tarar da Saudah a zaune ta zubawa kofar dakin Mama ido bata ko kiftawa wanda hakan ya tabbatarmun da ni ta ke jira. Na yi murmushi lokacin da na karasa wajenta tana zaune a kan doguwar kujera don haka na samu waje a kusa da ita na zauna. Na juya na fuskanceta da zummar yi mata magana sai kuma maganar Mahaifiyata ta fadomun.
“...ina son a cikin wadannan kwanakin ka nemi soyayyar Saudah ta amince da kai a matsayin mijin da za ta aura...”
Wani tattausan murmushi ne ya su6ucemun wanda ban san lokacin da na yi shi ba. Ni da BAN SAN SO BA ta ya zan iya neman soyayyar mace har ta amince da ni a cikin kwana uku?
“tunanin me ka ke yi Yayana?”
Saudah ce ta katsemun tunanin da na ke yi ta hanyar yimun magana. Na kalleta har a lokacin da sauran guntun murmushin a kan fuskata na ce,
“bakomai kanwata wata magana ce ta fadomun shi ne abun ya bani dariya”
Saudah ta yi murmushi sannan ta ce,
“nima fadamun na ji ka ji Yayana”
Na zazzaro ido ina kallonta na ce,
“ke sirri ne ba a son kowa ya ji”
Cikin shagwa6a Saudah ta ce,
“Yayana daman yanzu har a kwai wani sirri da za ka iya 6oyemun?”
na girgiza mata kai domin na gajarce tsayin surutun nata domin ta fara takuramun sannan na ce,
“yanzu dai je ki kawomun lemo mai sanyi na sha sai mu yi zancen”
Saudah ta yi murmushi sannan ta tashi ta nufi hanyar kitchen domin daukomin lemon kamar yadda na umarceta. Nikuwa daman na yi mata haka ne saboda ta tafi ni kuma na samu damar guduwa domin ina son kadaici, idan na ce ta kyaleni ba zata kyaleni ba ta cika takura ga surutu. Sai da na bari ta shiga kitchen din sannan na tashi da sauri na fita. Ummi ta bini da kallo tana dariya daman ta fahimci so na ke na gudu. Ban tsaya sauraronta ba ina ji ta na cewa “a dawo lafiya” na fita da sauri na shiga motata na tasheta na fita daga cikin gidan.
No comments:
Post a Comment